Rangers na fatan Miller zai sayi kulab din

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption magoya bayan Rangers

Masu gudanar da Kungiyar kwallon kafa ta Rangers sun bawa wani dan kasuwa a Amurka, Bill Miller, tayin kulab din kuma suna fatan kulab din zai kasance a hannunsa zuwa karshen kakar wasa.

Farkon tayin Miller din dai zai dogara ne akan Hukumomin kwallon kafa ta Scotland idan bata kara sa takunkumi kan kulab din ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Scotland da kuma Premier league na Scotland din dukkan su sun ce suna da muradin su tattauna da Miller.

Rangers dai na fuskantar takun kumin hana musayar 'yan wasa na tsawon watanni goma sha biyu kafin a daukaka kara kan hukuncin Kungiyar kwallon kafa ta Scotland din.

Karin bayani