Rashidi Yekini ya rasu

Asalin hoton, BBC World Service
Marigayi Rashidi Yekini
Rahotanni sun ce shahararren dan wasan kwallon kafar nan na Najeriya, Rashidi Yekini, ya rasu ranar Juma'a.
Dan wasan ya rasu ne yana da shekaru arba'in da tara, bayan ya jima yana fama da rashin lafiya.
Rashidi Yekini ya fara wasan kwallon kafa ne da kungiyar UNTL ta Kaduna, inda aka haife shi; ya kuma bugawa kungiyoyin cikin gida irinsu IICC Shooting Stars, da Abiola Babes, kafin ya koma Cote D'Ivoire, inda ya bugawa Africa Sports National.
Daga can ne kuma ya tafi Portugal inda hazakarsa a wasa ta bayyana sosai har ya zamo dan Najeriya na farko da ya samu kyautar gwarzon dan wasan Africa a shekarar 1993.