Afrika ta kudu ta zayyana filayen gasar Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gasar cin kofin Afrika

Kasar Afrika ta kudu ta zayyana biranen da za'a yi amfani da filayen wasannin su don gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afrika a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Garuruwan dai sun hada da Nelspruiet da rustenburg da Port Elizabeth da Durban da kuma Johannesburg.

Wannan matakin na nuna cewar filin wasan Cape Town da aka gina shi don gasar cin kofin Duniya na shekara ta dubu biyu da goma ba za ayi amfani da shi ba a wannan gasar.

Filin wasan Johannesburg wanda ada ake kira Soccer City a inda akayi wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya , anan ne za'ayi wasannin budewa da kuma na karshe.

Karin bayani