Ferguson, Mancini na sa ran cin gasar Premier

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto q
Image caption Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce yana fatan klub din Queens Park Rangers zai taimaka klub dinsa ya samu nasarar cin kofin gasar premier.

Ferguson ya bayyana fatan ne duk da cewa Manchester City na sama da klub dinsa kuma saura wasa daya a kammala gasar.

Sir Alex yace makomar klub dinsa ta dogara ne kaco kan a kan gasar, inda yayi fatan Mark Hughes na cikin masu buga kwallo.

Man City za ta kara ne da Queens Park Rangers a ranar karshe ta kakar wasannin.

Kuma Idan klub din yayi kunnen doki da Manchester United ko kuma ya dara sakamakon gasar Man U da Sunderlands,to Manchester City za ta dau kofi a karo na farko cikin shekaru 44.