Patrice yace manchester bata dena kakagida ba

Image caption Patrice Evra

Patrice Evra yace idan Manchester United ta kasa daukan kofin Premier a wannan karan ,hakan ba yana nufin kakagidan da take yi a gasar Premier din ta zo karshe ba ke nan.

Kyaftin din na Manchester yace ya kwana da sanin cewa idan basu dauki kofin Premier din ba a wannan karan mutane da yawa zasu ce ai karshen kakagidan da mukeyi a Premier shike nan ya kare ,suce yaya zamu karke kenan ai tamu ta kare, to amma abin ba haka yake ba domin akwai gwanayen 'yan wasa da yawa a nan.

Patrice Evra yace, al 'amarin ya zo mana da bazatta mun yi fama da matsalar raunin 'yan wasa ga shi kuma mun rasa kwararrun 'yan wasa da suka fice daga kulob din a bazarar da ta wuce ,duk wannan ba abu ne da zamu iya shawo kansu cikin sauki ba.

Idan da Manchester United din zata dauki Premiern a wanna karon ma to da karo na 20 ke nan ta dauka.

Karin bayani