Ana binciken sama da kungiyoyi 20 a Italiya

Hakkin mallakar hoto AP

An shaidawa sama da kungiyoyin kwallon kafa 20 a Italiya cewa ana bincikensu saboda zargin siyarda wasa.

A yanzu haka dai ana tsare da sama da mutane 30 bayan bincike game da badakalar a shekarar da ta gabata a Italiya.

Masu shigar da kara dai na zargin anyi coge a wasanni 33.

Binciken dai ya kara bullo da wani sabon babi a harkar kwallon kafa a kasar, kamar yadda ya faru a shekara ta 2006, inda aka maida kungiyar Juventus zuwa matsayi.