NFF ta sauya filayen wasa saboda tsaro

Hukumar kwallon kafan Najeriya, wato NFF ta sauyan filayen wasan da za'a buga wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da na Afrika saboda fargabar tsaro.

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar a ranar alhamis ta ce wasanni da tawagar Super Eagles za ta buga da Namibia da kuma Rwanda za'a buga su ne a garin Calabar da ke kadu maso gabashin kasar.

Hukumar dai ta ki a buga wasannin ne a babban filin wasa na Abuja, saboda akwai matsala da ciyawar filin.

A baya dai an shirya za'a buga wasannin a jihar Kaduna, amma jihar na fama da matsalar tsaro.