Ana tuhumar Wilkins da tuki cikin maye

Tsohon kocin Chelsea, Ray Wilkins
Image caption Tsohon kocin Chelsea, Ray Wilkins

Tsohon tauraron wasan kwallon kafa na klub din Chelsea da kuma Manchester United Ray Wilkins zai gurfana a gaban kuliya bisa zarginsa da laifin tuki cikin maye.

An kama Wilkins ne a kusa da gidansa dake Cobham a Surrey da jijjibin safiya ranar litinin data gabata a cewar 'yan sanda.

Mr. Walkins mai shekaru 55 wanda ke yin sharhin wasannin kwallo da gidan talabijin na Sky kuma tsohon kocin Chelsea ya fuskanci tambayoyi a ofishin 'yan sanda dake Reigate.

An bada bailinsa bayan an tuhume shi, sannan zai gurfana a gaban kotun majistire dake Surrey a ranar 21 ga tawan Mayu.