Harry Redknapp ya musanta sayar da Bale

Harry Redknapp Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Kungiyar wasan kwallon kafa ta Tottenham Harry Redknapp ya musanta yarjejeniyar sayar da Gareth Bale ga Bercelona kan kudi fan miliyan 32.

Rahotanni daga kafafen yada labaran Spain sun nuna cewar Bercelona sun shirya biyan euro miliyan 40 domin sayen dan wasan tsakiyar mai shekaru 22.

"Ba na tunanin akwai kanshin gaskiya a kan wannan batu," inji Redknapp.

Ya kuma kara da cewar ''Ko kun san cewar an zabi Bale a tawagar gasar wasan Premier na shekara?''

Kocin kungiyar ta Tottenham ya kara jaddada cewar kungiyar ta arewacin birnin London na son adana kwararrun 'yan wasanta domin samun nasarar shiga gasar zakaru a koda yaushe.

Karin bayani