Ferguson ya taya City murnar cin Premier

Sir Alex Ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson ya taya Manchester City murna

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya taya Manchester City murna a bisa nasarar da ta yi ta lashe Gasar Premier da yawan kwallaye.

Sai dai kuma kocin ya yi gargadin cewa a kakar wasanni ta badi, United za ta dawo da karfinta don yin fatafata da abokan karawarta.

"A madadin Manchester United ina taya Manchester City murna saboda lashe Gasar Premier da ta yi", in ji Ferguson.

Ya kuma kara da cewa: "Ba abu ne mai sauki ba a lashe Gasar Premier, don haka duk wanda ya lashe ta to lallai ya cancanta saboda aiki ne ja".

Da an tashi a wasannin da aka buga ranar Lahadi a yadda sakamako ya kasance a minti na casa'in, da United ce ta lashe Gasar—a daidai lokacin dai United ta ci Sunderland daya ba ko daya, yayinda City ta sha kashi a hannun QPR da ci biyu da daya.

Sai dai kuma ana daf da tashi a wasan City ta ci kwallaye biyu.

Maki tamanin da taran da United ke da shi ne maki mafi yawa da kungiyar da ta zo ta biyu a teburin Gasar Premier ta samu a kakannin wasanni ashirin.

Ferguson ya kuma ce 'yan wasa da magoya bayan City na da damar yin murna yadda suka so, amma kuma United ta yi fice saboda ta jima da kafa tarihi.

"Mu ba abin da zai dame mu; ina ganin muna da dimbin tarihi, mun ma fi kowa tarihi, kuma sai sun yi shekaru dari kafin su kafa tarihi irin namu", in ji Ferguson.

Karin bayani