Ruud van Nistelrooy yayi Ritaya

Ruud van Nistelrooy ya yi ritaya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ruud van Nistelrooy ya yi ritaya

Tsohon dan wasan Manchester United, Ruud van Nistelrooy, dan shekara 35 ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa.

Dan wasan, dan kasar Holland,da yake yiwa kungiyar Malaga ta Spain wasa ya kasance cikin wani hali mai wuya a kakar wasannin bana inda ya sami damar cin kwallaye 5 kawai a wasanni 35.

Daman kwantiraginsa da kungiyar ya zo karshe, kuma ya bayyana a wasansa na karshe da kungiyar tayi da Gijon inda suka sami nasara da 1-0 cewa wasansa na karshe ke nan.

A karshen wasan yace wannan shi ne wasansa na karshe a rayuwarsa ta sana'ar kwallon kafa.

Yace yayi fatan ya buga gasar zakarun Turai ,amma hakan ba zata yuwu ba ,lokacine na ya bar wasan haka.

''Na zo karshen iya abinda zan iya yi kuma ba zan iya wasan da ya wuce haka ba.Ba wani lokaci da yafi dacewa na dakata da wasa kamar yanzu'' inji shi

Yace yayi farin ciki cewa shi ne da kansa yake yanke wannan shawara.

Ya ce ya godewa kungiyar Malaga da sauran jami'anta akan shekarar da ba zai taba mantawa da ita ba.

Shi dai Van Nistelrooy, ya yiwa kasarsa Holland, wasa har sau 70, inda ya ci kwallaye 35. Ya fara wasansa da kungiyar Den Bosch,inda ya yi shekara 5 kafin ya koma kungiyar Heerenveen.

Daga nan a shekara ta gaba ya koma PSV Eindhoven, inda kungiyar ta sami nasarar lashe gasar rukuni har sau 2, wanda hakan yasa yayi suna a kasarsa ta Holland.