Villa ba ta kyautawa McLeish ba —Atkinson

Alex McLeish Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Litinin Aston Villa ta kori Alex McLeish

Tsohon kocin Aston Villa, Ron Atkinson, ya ce ba a baiwa kocin da kungiyar ta kora, Alex McLeish, dama ya yi nasara ba.

An kori kocin ne ranar Litinin, bayan kungiyar ta Aston Villa ta kammala Gasar Premier a matsayi na goma sha-shida a kan tebur; kuma wasanninta na gida hudu kacal ta ci.

Atkinson ya shaidawa BBC cewa "Tun daga ranar farko yake cin karo da matsaloli. Ina ganin saboda ya fito ne daga Birmingham.

"Ina ganin ba a kyauta masa ba".

Atkinson, wanda ya horar da 'yan wasan kungiyar tsakanin shekarar 1991 da 1994 ya kuma kai ta matsayi na biyu a teburin Gasar Premier a kakar wasannin gasar ta farko—1992-1993—ya kuma kara da cewa ba a baiwa McLeish 'yan wasa da kudaden da yake bukata don ya kawo sauyi a Villa ba.

"Suna bukatar taurarin 'yan wasa, saboda 'yan kallo na so su ga 'yan wasan da za su sa hutunsu na karshen mako ya yi armashi", in ji Atkinson.