Mancini: City za ta yi koyi da Madrid, Barca

Mancini da kofin Premier Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mancini da kofin Premier

Roberto Mancini: Man City zata yi koyi da Real Madrid da Barcelona.

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya yiwa magoya bayan kungiyarsa alkawarin cewa kungiyar zata kashe kudi kamar kungiyoyin Barcelona da Real Madrid a wannan bazarar domin samun nasarar daukar kofin Champions League.

Mancini ya shedawa BBC cewa, kowace shekara Barcelona da Real Madrid suna sayen 'yan wasa biyu ko uku kuma su kashe makudan kudade.

'' ina ganin haka zata kasance ga Manchester City ma'' inji Mancini.

Yace muna bukatar mu kara karfi, muna bukatar mu sami karfin da zamu iya tunkarar wasan zakarun turai da kuma gasar Premier.

Mancini, ya kara da cewa domin cimma wannan buri muna bukatar kyakkyawar kungiya mai karfin gaske da 'yan wasa masu kaifin basira da maida hankali kan abinda ake bukata kuma na tabbata zamu iya yin hakan.

Karin bayani