Ba zan yi ritaya ba yanzu - Micheal Owen

Micheal Owen Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Micheal Owen

Micheal Owen, ya ce ba shi da shirin yin ritaya daga wasa, duk da cewa Manchester United ta ce ba za ta sabunta kwantiraginta da shi.

Dan wasan mai shekara 32, ya ce zai zauna na wani dan lokaci ya duba abinda zai yi a gaba, amma ko alama ba shi da aniyar barin fagen kwallon kafa a yanzu domin ba ya jin ya kai lokacin da ba zai iya cin kwallo ba a matakin koli na wasan.

Tsohon dan wasan gaban na Ingila ya ce duk da cewa ya dan yi fama da matsalar raunuka daga lokaci zuwa lokaci ,duk da haka ba ya tashi yaji jikinsa ko wata gaba ta jikinsa tana ciwo.

An shedawa tsohon dan wasan na Liverpool da Real Madrid da Newcastle matakin kin sabunta kwantiragin nasa da Manchester United din ne a lokacin wasan girmama tsohon mai tsaron gidan United din Harry Gregg, a Belfast ranar Talata.

Karin bayani