Tawagar Chelsea ta kewaya titunan London

'yan wasan Chelsea Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tawagar 'yan wasan Chelsea na murna

Dubban magoya bayan Chelsea ne suka yi tururuwa kan titunan yammacin London, su na yabawa 'yan wasan kungiyar da suka lashe kofin zakarun turai.

Tawagar kungiyar wadda ke cikin motocin safa safa biyu marassa rufi ta fara zagayen ne tun daga filin wasan kungiyar na Stamford Bridge har zuwa Parsons Green. Ta ko ina ba abinda ake gani sai magoya bayan kungiyar wasu makalkale a jikin fitilun gefen titi dauke da tutar kungiyar mai launin shudi da fari.

'yan wasan dai sun gabatar da jawabai ga magoya bayan nasu yayinda magoya bayan ke ta rera wakokin nasara da yabawa 'yan wasan da sauran shugabannin kungiyar ta Chelsea.

Haka kuma magoya bayan Chelsea din sun rinka rera wakar taya murnar zagayowar ranar haihuwar mai tsaron gidan kungiyar Petr Cech da Didier Drogba.

Wannan dai shi ne karon farko da wata kungiyar kwallon kafa daga London ta sami nasarar daukan kofin na zakarun turai.