Chelsea na duba yuwuwar baiwa Di Matteo cikakken koci

Roberto Di Matteo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Chelsea Di Matteo

Shugaban Chelsea Bruce Buck ya ce kungiyar ta na duba yuwuwar baiwa Roberto Di Matteo matsayin cikakken kociyan ta bayanda ta sami nasarar cin kofin zakarun turai.

Mr Buck ya ce kocin wanda ke zaman na wucin gadi a yanzu, ya yi kokari matuka .

Ya farfado da kungiyar, a don haka babu makawa kungiyar ta na matukar duba yuwuwar tabbatar ma sa cikakken mukamin mai horadda da 'yan wasan nan ba da dadewa ba, kafin lokacin musayar 'yan wasa.

Di matteo, dan shekara 41 wanda tsohon kocin kungiyar MK Dons da West Brom ne, ya sami cigaba ne daga mukamin mataimakin koci zuwa mai rikon kwarya a kungiyar ta Chelsea bayan da tsohon kocin ta Andre Villas-Boas ya kasa tabuka komai a kungiyar.

Tauraron Di Matteo ya kara haskakawa sosai sakamakon wannan nasara da ya samu ta kai ga kungiyar Chelsea din ga daukan kofin zakarun turai wanda a makwanni biyu da suka wuce kungiyar ta dauki kofin kalubale ,FA na Ingila.

Karin bayani