Didier Drogba ya bar Chelsea

Didier Drogba Hakkin mallakar hoto
Image caption Didier Drogba ya taimakawa Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai

Kungiyar Chelsea ta tabbatar da cewa Didier Drogba ya bar kulob din bayan ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai.

Drogba zai bar kungiyar ne a karshen watan Yuni mai zuwa bayan shafe shekaru takwas.

Dan wasan na kasar Ivory Coast mai shekaru 34, wanda ya buga fanaretin da ya baiwa Chelsea damar lashe gasar zakarun Turai, zai tafi ne a kyauta bayan da kwantiraginsa za ta kare a watan gobe.

Bayan shafe watanni ana rudani kan makomarsa, Drogba ya tabbatar da cewa zai tafi:

"Ina so na kawo karshen cece-kuce a kaina, don haka na tabbatar da cewa zan bar Chelsea," kamar yadda ya shaida wa shafin internet na kulob din.

Karin bayani