Mace ta farko a kwamitin gudanarwar Fifa

Mace ta farko a kwamitin gudanarwar Fifa
Image caption Ita ce mace ta farko da za ta shiga kwamitin gudanarwar Fifa

Shugabar hukumar kula da kwallon kafa ta Burundi, Lydia Nsekera, za ta zamo mace ta farko mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.

Za a shigar da ita cikin babban kwamitin na Fifa a babban taron da Fifa za ta yi ranar Juma'a.

Dama dai mamba ce a kwamitin shirya gasar kwallon kafa na Olympic, kuma tana cikin kwamitin kwallon kafa na mata na hukumar ta Fifa.

Za a samu zababbiyar wakiliya mace a kwamitin daga shekara ta 2013.

Nsekera mamba ce kuma a kwamitin gudanarwa na gasar Olympic na duniya.

Ta kasance a shugabancin hukumar kwallon Burundi tun daga shekara ta 2004, kuma ita ce mace ta biyu da ta shugabanci hukumar kwallon kafa a Afrika - bayan Sombo Izetta Wesley ta kasar Liberia.

Matakin na sanya mace a kwamitin zartarwar wani bangare ne na sauye-sauyen da Fifa ke gudanarwa, biyo badakalar da ta taso lokacin bayar da izinin shirya gasar cin kofin duniya ta 2018 da 2022.