Jenson Button na kan gaba a Monaco

Jenson Button Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A ranar Asabar za a gudanar da zagaye na biyu na tseren

Direban McLaren Jenson Button, ya zamo kan gaba a zagayen farko na gasar tseren motoci ta Grand Prix a birnin Monaco.

Dan wasan na kasar Ingila, na daya daga cikin tsirarun direbobin da suka yi tazara, kafin ruwan sama ya barke na tsawon mintina 15.

Tunda farko Fernando Alonso na Ferrari ne ya kasance kan gaba a tseren farko.

Sai dai ruwan saman da ya barke ya kawo tsaiko ga ci gaban tseren.

Button, wanda abokin tserensa Lewis Hamilton ya zo na 11, ya ce: "Yana fatan za a samu yanayi mai kyau ranar Asabar, bayan da aka samu tsaiko a ranar Alhamis."

Sai dai kashi 80 cikin dari na hasashen yanayi ya nuna cewa akwai yiwuwar ayi ruwan sama.