Kalou da Bosingwa na shirin barin Chelsea

Salomon Kalou Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Salomon Kalou ya zira kwallaye 60 a wasanni 250

Rahotanni sun ce Chelsea na shirin sallamar Salomon Kalou da Jose Bosingwa idan kwantiraginsu ta kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Nan gaba kadan ne kulob din zai fayyace sunayen 'yan wasan da zai ci gaba da zama da su, kuma ana saran babu sunayen Kalou, da Bosingwan da kuma Drogba wanda tuni ya bayyana aniyarsa ta barin kulob din.

Kalou, dan shekaru 26, ya zo Chelsea ne daga Feyenoord a shekara ta 2006 kan kudi fan miliyan 8. Yayin da Bosingwa, mai shekaru 29, an sayo shi ne kan fam miliyan 16 daga FC Porto a 2008.

Bosingwa, ya taka leda sau 127 a Chelsea, yana da damar sabunta kwantiraginsa da shekara daya, amma kulob din baya so ya karbi karin.

Yayin da shi kuma Kalou, ya taka leda fiye da sau 250 inda ya zira kwallaye 60.

Florent Malouda, da Michael Essien da kuma Paulo Ferreira duka na da sauran shekara guda a kwantiraginsu, kuma ana saran tattaunawa da su kan yiwuwar sabunta ta.

Karin bayani