Campbell ya gargadi 'yan kallo a kan Euro 2012

Sol Campbell Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon kyaftin din Ingila Campbell

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ingila Sol Campbell ya gargadi 'yan kallo a kan ka da su kuskura suje wurin wasan gasar cin Kofin kasashen Turai ta Euro 2012 da za a yi a Poland da Ukraine saboda fargabar fuskantar harin wariyar launin fata.

Tsohon dan wasan yace tun farko ma bai kamata ce am baiwa kasashen damar karbar bakuncin wasan ba saboda kaurin suna da su ka yi na tashin hankali da nuna wariya.

Campbell ya ce shawarar sa ga masu sha'awar kallon ita ce su zauna a gida kawai su kalli wasan. ka tsaya a gida kawai ka kalli wasan a talabijin.

Kada ma ka yi kuskuren jarraba zuwa saboda kana iya dawowa a makara.

To sai dai a martanin da ya mayar game da kalaman na Campbell tsohon dan wasan Ukraine Shevchenko cewa ya yi ba su da wata matsala a kasar wadda ta danganci bambancin launin fata.

Ya ce mutanen kasar jama'a ne da ba su da hayaniya kuma masu faran-faran da kowa ne

Karin bayani