Tenis: Robson ta sha kashi a hannun Garrigues

Laura Robson
Image caption Laura Robson

Laura Robson ta sha kashi a hannun Anabel Medina Garrigues a karawarta ta farko a gasar tenis ta French Open.

'Yar wasan ta Burtaniya mai shekaru goma sha takwas da haihuwa ta samu shiga gasar ne bayan Silvia Soler-Espinosa ta janye.

Sai dai kuma ba ta jima a gasar ba, saboda Medina Garrigues ta lallasa ta da ci shida da biyu da kuma shida da daya a cikin sa'a daya da minti goma.

Sauran 'yan kasar Burtaniyar da suka saura a gasar—Andy Murray, da Anne Keothavong, da Heather Watson—sai ranar Talata za su yi wasanninsu na farko.