Brendan Rogers zai jagoranci Liverpool

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran tabbatar da Brendan Rodgers a matsayin kocin Liverpool

Ana sa ran nan da sa'o'i arba'in da takwas masu zuwa, za a tabbatar da kocin Swansea, Brendan Rodgers, a matsayin sabon kocin Liverpool.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyoyin biyu [Swansea da Liverpool] na tattaunawa a kan abin da za a bayar; mai yiwuwa Swansea ta karbi abin da ya kama daga fam miliyan hudu zuwa biyar a matsayin diyya.

An jima ana tunanin kocin Wigan Roberto Martinez za a baiwa matsayin, amma tuni aka sauya shawara aka mayar da hankali a kan Rodgers.

An kuma bayar da rahoton cewa kungiyar ta Liverpool za ta kuma nada daraktan kwallon kafa.

Rahotanni dai sun nuna cewa a da kungiyar tana yunkurin nada wani mutum kamar Johan Cruyff ko Louis van Gaal da kuma koci, amma ga alama yanzu Rodgers ne kadai zai jagoranci kungiyar.

Ranar 16 ga watan Mayu ne dai Liverpool ta sallami Kenny Dalglish, bayan ta kare kakar wasanni ta bana a matsayi na takwas a kan teburin Gasar Premier.

Karin bayani