Usain Bolt ya yi nasara a Rome

Usain Bolt Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Usain Bolt

Dan wasan tseren mita 100 na kasar Jamaica Usain Bolt ya sake komowa kan ganiyarsa inda ya kammala gudun a cikin dakika 9.76 a gasar tseren a birnin Rome na Italia.

Wananan shi ne gudu mafi sauri da aka yi a wannan shekara a tseren mita darin.

A ranar Juma’a da ta wuce dan tseren na Jamaica ya yi nawa inda ya kammala tseren a cikin dakika 10.04 a Ostrava ta jamhuriyar Czech.

Amma a wannan karon Usain Bolt ya farfado inda ya tserewa takwaransa dan kasar Jamaica Asafa Powell wanda ya zo na biyu a cikin dakika 9.91, da kuma Dan Faransa Christophe Lemaitre wanda shi kuma ya kammala tseren da dakika 10.04

Bolt ya bayyana jin dadinsa ganin yadda ya dawo kan ganiyarsa ta yin fintinkau atseren mita 100.