'Cahill da Terry za su taka leda a gasar Euro'

Hakkin mallakar hoto Getty

Direktan habbaka wasanni a Hukumar kwallon Ingila wato FA, Sir Trevor Brookings ya ce yan wasan bayan kasar biyu wato Gary Cahill da John Terry za su taka leda a gasar Euro da za a fara a mako mai zuwa.

An dai duba lafiyar yan wasan biyu bayan raunin da su ka samu a wasan sada zumunci da kasar ta buga da Belguima a ranar asabar.

Ingila dai ta yi nasara a wasan da ta buga da Belguim da ci daya mai ban haushi.

"Rahotannin da muke samu na cewa raunin da su ka samu bai yi muni ba." In ji Brooking.

Kocin Ingila Roy Hodgson na fama da rashin manyan 'yan wasa saboda raunin.

'Yan wasan da su ka fice daga tawagar Ingila saboda rauni sun hada mai tsaron gida, John Ruddy da yan wasan tsakiya Gareth Barry da Frank Lampard.

Brooking ya shaidawa BBC cewa yana da kwarin gwiwa Cahill da Terry za su murmure kafin an fara gasar.