Chelsea ta sayi Eden Hazard

Kungiyar Chelsea dake Ingila ta kammala cimma yarjejeniyar siyan Eden Hazard daga kungiyar Lille ta Faransa.

Dan wasan wanda dan asalin Belgium ne ya amince da yarjejeniyar da kungiyoyin biyu su ka cimma, kuma har ma an duba lafiyarsa.

"Zai dawo kungiyar ne a watan Yuli, idan 'yan wasan sun fara horo fara kakar wasa." In ji Sanarwar da Chelsea ta fitar a shafinta.

Hazard ya ce: "Ina matukar murna da komawa Chelsea, babbar kungiya ce, kuma duk na zaku in fara taka mata leda."