Kamaru ta baiwa Lavagne kwantaragi

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwammnatin Kamaru ta baiwa Denis Lavagne kwantaragi bayan nasarar da Kamaru ta yi a kan Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da ci da nema a ranar asabar.

Kasashen biyu sun taka leda ne a wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014.

A baya dai Hukumar kwallon kasar ne ke biyan kocin albashi tun da ya karfi aiki daga Javier Clemente a ranar 29 ga watan Nuwamba.

An dai nada Lavange ne domin ya dawo da martabar kwallon kafa a Kamaru wadda ba ta samu halatar gasar da aka shirya a Equatorial Guinea da Gabon ba a watan Junairun da ya gabata.