'Ana kokarin batawa Hodgson suna'- Eriksson

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Sven-Goran Eriksson

Tsohon kocin Ingila, Sven-Goran Eriksson ya ce ana batawa kocin kasar na yanzu, wato Roy Hodgson suna saboda bai sanya sunan Rio Ferdinand ba a jerin 'yan wasan da zasu taka leda a gasar Euro.

Tun da farko dai ba'a sanya sunan Ferdinand ba, sannan bayan Gary Cahill ya samu rauni aka kara watsi fa shi, inda aka sanya sunan dan wasan Liverpool Martin Kelly.

"Zaban Kelly da kocin ya yi ya sanya mutanen sun sa shi a gaba." In ji Eriksson.

"Bayan ya zabi 'yan wasan Liverpool shida mutane da dama na ta zaginsa."

Eriksson ya ce yana da kwarin gwiwa Hodgson zai iya fuskantar kalubalen sukarsa da ake ta yi.

Hodgson dai ya ce rashin sanya sunan Ferdinand cikin 'yan kwallon Ingila, ba son zuciya bane illa an yi hakan ne saboda dalilai da su ka danganci kwallon kafa.

Akwai dai wadanda su ke zargin cewa ba'a kira dan wasan bane saboda kada a samu rashin jituwa da John Terry wanda zai gurfana a gaban kotu kan zargin kalamun wariyar launin fata da ya yiwa dan uwan Ferdinand wato Anton.

Terry dai ya musanta zargin.