Kocin Zambia ya fusata da gwamnatin kasar

Hakkin mallakar hoto

Kocin Zambia, Herve Renard ya nuna rashin jin dadinsa game da irin shirin da gwamnatin kasar ta yi kafin tattakin da kasar ta kai Sudan domin taka leda.

Zambia dai ta sha kashi ne a hannu Sudan da ci biyu da nema a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekara ta 2014.

Tawagar Zambia dai ta samu matsalar samun jirgin saman da zai kai su Sudan a yayinda ana sauran kwana daya ne a buga wasan su ka isa kasar a jirgin kasuwa.

Renard dai ya so tawagar kasar ta taso daga kasar Afrika ta kudu inda su ka yi horo a jirgin Chatter.

"A kwallon kafa ya kamata ka nuna kwarewar ka. Mu ba kwararru bane." In ji Renard.

"Bana son ina aiki haka. Ba zan iya ci gaba da aiki haka ba, idan mutane basa so su yi aiki da kwararre kama na."

Amma har wa yau kocin ya ki alakanta rashin nasarar da kasar ta fuskanta ga rashin samun jirgin cikin.