Tiger Woods ya yi nasara a wasan golf

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tiger Woods

Tiger Woods ya yi nasara a wasan golf na Memorial ta bana kuma wannan shi ne kambunsa na biyu a bana.

Yanzu dai Woods na kafada - kafada da Jack Nicklaus me dauke da kambu 73.

Da aka nemi ra'ayinsa game da wanan sakamako Woods ya ce " Wannan muhimiyar ranace a gare ni saboda nasarar da na yi kuma ga shi Jack na wurin. Mutum ne da yan wasa su ka dauka da muhimanci."

Nasarar da Woods ya yi ta biyo bayan wadda ya yi a wasan golf na Arnold Palmers da aka yi a watan Maris, abun da kuma ya kawo karshen koma bayar da ya ringa fuskanta a rayuwarsa da kuma raunukan da ya samu.