Mikel Arteta ya nemi Arsenal ta karamasa albashi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mikel Arteta

Shugaban kungiyar kwallon kafa na Arsenal Ivan Gazidis zai gana da wakilan Mikel Arteta a makon da mu ke ciki domin su tattauna akan yadda zaa inganta kwantragin dan wasan tsakiyar.

Arteta me shekaru 30 na karban fam dubu 10 a kowani mako kafin ya bar Everton akan kudi euro miliyan goma a kakkar bara.

Dan wasan tsakiya ya sa hanu akan yarjejeniyar shekaru hudu akan fam dubu 60 a kowani mako kuma ya nemi kungiyar akan ta sake yin nazari akan kwantaraginsa biyo bayan nasarorin da suka samu a kakkar bana.

Areteta ya zira kwallaye shida a wasani talatin da takwas a karawar da Arsenal tayi.