An nada Chris Hughton a matsayin kocin Norwich City

Hakkin mallakar hoto Getty

Norwich City ta nada kocin Birmingham City, Chris Hughton a matsayin kocinta.

Tsohon kocin Newcastle din Hughton, mai shekarun haihuwa 53, ya jagoranci Birmingham ne tun daga watan Yunin shekara ta 2011, kuma ya maye gurbin Paul Lambert ne wanda ya koma Aston Villa.

Kocin wanda tsohon dan wasan Tottenham ne da kasar Jamhuriyar Ireland, ya jagoranci Birminghan zuwa wasan kusa da na karshe a wasanni kokari tsallake zuwa gasar Premier daga Championship.

Hughton ya ce: "Wannan abun farin ciki ne a gare ni, kuma na zaku in fuskanci kalubalen dake gabana.

"Paul ya yi gaggarumin aiki a nan, kuma dolene in dora a kan abun da ya bari."