Kocin Villareal ya rasu bayan sa'o'i 24 da nada shi

Tsohon kocin Sporting Gijon Manuel Preciado mai shekarun haihuwa 54 ya rasu sanadiyyar bugun zuciya.

Kocin ya rasu ne sa'o'i 24 bayan ya amince ya jagoranci kungiyar Villarreal a kakar wasanni ta 2012-13.

An dai ragewa Villarreal matsayi ne a kakar wasan bara daga gasar Laliga ta Spaniya.

Kungiyar Sporting Gijon ta sallami Preciado a watan Junairu bayan ya taimakwa kungiyar tsallakowa zuwa gasar Laliga sau biyu bayan an rage mata matsayi.