An nada Steve Bruce a matsayin sabon kocin Hull City

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Steve Bruce da Asemoah Gyan

Hull City ta nada tsohon kocin Sunderland Steve Bruce a matsayin sabon kocin kungiyar na tsawon shekaru uku.

A watan daya gabata aka kori kocin Hull City Nick Barmby.

Bruce ya taba jagorantar Wigan da Birmingham a gasar frimiya , kuma ya kasance ba shi da aikin yi tun bayan lokacinda Sunderland ta kore shi a watan nuwamba bara.

An dai kori Barmby a matsayin kocin Hull City a filin wasa na KC saboda wasu kalaman da ya aiwatar ga manema labaru.