Poland ta yi kunnen doki da Girka

Poland ta yi kunnen doki da Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne wasa na farko a gasar ta bana

Daya daga cikin masu masaukin baki Poland ta tashi daya-da-daya tsakaninta da Girka a wasan farko na gasar cin kofin kasashen Turai na Euro 2012.

Robert Lewandowski ne ya fara zirawa Poland kwallonta a minti na 17 da fara wasan.

Sannan kuma aka baiwa Sokratis Papastathopoulos na Girka jan kati kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Dimitris Salpingidis ne ya farkewa Girka bayan ya shigo wasan daga benci.

Daga bisani kuma ya samo fanareti bayan da golan Poland Wojciech Szczesny, ya kayar da shi - abinda ya sa aka bashi jan kati.

Sai dai Giorgos Karagounis ya barar da fanaretin bayan da gola Przemyslaw Tyton ya kade kwallon.

Wasan wanda shi ne na farko a gasar ya kayatar sosai.

Karin bayani