Jamhuriyar Czech 2 Girka 1

Hakkin mallakar hoto AP

Jamhuriyar Czech ta farfado da damar ta ta tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin Turai bayan ta yi nasara a kan Girka da ci biyu da daya.

Jamhuriyar Czech dai ta zura kwallayen ne cikin mintina shida da fara wasan.

Petr Jiracek ne ya fara zura kwallon farko ana minti uku da fara wasan a yayinda Vaclav Pilar ya zura ta biyu.

Girka dai ta zura kwallon da a ka hana a wasan saboda a yi zargin dan wasanta na satan gola, amma bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Fanis Gekas ya zura kwallo a ragar Jamhuriyar Cezch bayan da mai tsaron gidanta Petr Cech ya yi aman kwallon.

Cezch dai ta sha kashi a wasan farko da ta buga da Rasha da kwallaye hudu da daya a yayinda kuma Girka ta buga kunnen doki da Poland.