Hodgson na fargabar rashin nasara

Kocin Ingila Roy Hodgson Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Ingila Roy Hodgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila Roy Hodgson ya tabbatar da cewa irin cikas din da Kungiyarsa ta fuskanta a wasannin baya na cusa wa 'yan wasansa fargaba.

Hakan na faruwa ne yayin da Ingilar ke shirin karawa da kasar Faransa, Litinin din nan, a gasar cin Kofin nahiyar Turai ta wannan shekarar.

Wannan karawar da Ingila za ta yi da Faransa ita ce wasa na farko da Hodgson zai jagoranta da suna shiga wata gasa tun da ya karbi ragamar horar da Kungiyar Kwallon kafa ta Ingila daga hannun Fabio Capello.

Hodgson ya ce nasarorin da Ingila ta samu a gasanni da dama ba su kai yawan da aka tsammanta mata ba, kuma wannan fargabar na zukatan 'yan wasan.

A cewarsa, 'yan wasansa ba su da wata mafita sai sun cire fargabar faduwa a zukatansu, sun yi wasa gaba-gadi.