Croatia ta rike Italiya inda suka tashi 1-1

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mario Mandzukic ya fanshe kwallon da Italiya ta zura a ragar Croatia a wasan da kasashen biyu su ka tashi daya da daya a wasan da su ka buga a rukunin C a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Croatia dai na bukatar maki uku kafin wasan domin tsallakewa zuwa zagaye na gaba, bayan nasarar da ta yi a wasan farko a kan Jamhuriyar Ireland da ci uku da daya.

Italiya ce dai ta mamaye wasan kafin kwallon farko da Andrea Pirlo ya zura a minti 39 a bugun falan daya.

A yanzu haka dai Italiya na da maki daya, kuma akwai yiwuwar idan ta yi nasara a wasanta na karshe da Jamhuriyar Ireland sannan ta tsallake zuwa zagaye na gaba.

Croatia ma dai a bukatar nasara a kan Spain ne a wasanta na karshe domin tsallakewa zuwa wasan dab da kusa dana karshe.