Portugal ta sha da kyar a hannun Denmark

Hakkin mallakar hoto Reuters

Portugal ta doke Denmark da ci uku da biyu a wasan da kasashen biyu su ka buga a rukunin B a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Pepe ne ya fara sanya Portugal a gaba ana minti 25 da fara wasan.

Bayan minti 36 ne kuma Postiga ya zura ta biyu

Denmark dai ta dawo da karfinta daga baya, inda Niclas Bendtner ya fanshe kwallo daya ana sauran mintuna hudu a tafi hutu rabin lokaci, kuma an an dawo ana sauran minti goma a tashi wasan ya fanshe kwallo ta biyu.

Silvestre Varela wanda ya shiga wasan daga baya ya taimakwa Portugal ana sauran mintuna uku a tashi wasan.