Roger Milla ya nemi da a kwantar da hankali

Hakkin mallakar hoto Getty

Shaharraren dan kwallon kafan nan a Kamaru wato Roger Milla ya nemi magoya bayan kwallon kasar da su kwantar da hankalinsu bayan an kaiwa dan wasan kasar Alex Song hari.

Magoya bayan kasar dai sun fusata ne bayan kashin da kasar ta sha a hannun Libya a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekara ta 2014.

Milla ya nemi, magoya bayan kasar sun kwantar da hankalinsu a wani jawabi da ya yi a gidan rediyon kasar.

Ya bukace su da su nuna goyon baya ga tawagar kasar dari bisa dari a yayinda take shirin tunkarar Guinea Bissau a karshen mako a wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin da za'a shirya a shekarar 2013.

Kamaru dai tana kan gaba ne da ci daya da nema a bugun farko.

Kwallon kafa a Kamaru na fuskantar koma baya abun da kuma ya sanya aka tube Roger Milla a mukaminsa na shugaban hukumar kwallon kasar saboda sukar da yake yi kan wadanda aka daurawa alhakin tafiyar da harkar kwallon kafa a kasar.