Redknapp na tsaka-mai-wuya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham, Harry Rednapp, na fuskantar kalubale na yiwuwar barin kulab din duk da cewa ya sha musanta yiwuwar hakan.

Redknapp, mai shekaru 65, zai gana da shugaban kulab din, Daniel Levy, a ranar Laraba inda za su tattauna game da makomarsa a kulab din.

Mutanen biyu ba sa jituwa da juna.

Wa'adin Redknapp zai kare ne a watan Yunin 2013.

Ana ta jita-jitar yiwuwar ajiye aikinsa.

Ya ce; '' Ban sauka daga mukamina ba.Ban san abin da yasa mutane ke ta cece-kuce a kan wannan batu ba. Abin da mutane ke yi( jita-jita) bai dace ba''.

Tottinham ya lashe hudu daga cikin wasannin karshe da ya buga a gasar Firimiya, inda ya ci biyar a wasan da suka buga da Arsenal, yayin da Arsenal ya ci biyu.

Karin bayani