Spain ta fidda Jamhuriyar Ireland a gasar Euro

Hakkin mallakar hoto Reuters

Fernando Torres ya zura kwallaye biyu a yayinda Spain ta fidda Jamhuriyar Ireland a gasar cin kofin Turai bayan ta doke ta da ci hudu da nema.

Torres ya zura kwallo farko ne bayan ya cillo ta daga yaddi goma ana minti hudu da fara wasan.

Bayan kuma an dawo hutun rabin lokaci ne kuma David Silva ya zura ta biyu sannan Fernando Torres ya zura ta uku.

Cesc Fabregas wanda ya sauya Fernando Torres ne ya zura kwallo ta hudu.

A yanzu haka dai Spain ce ke jagoranci a rukunin C, yayinda Croatia ke biye da ita, kuma kasashen biyu na da maki hudu ne kowannensu.

Spain dai za ta hadu ne da Croatia a ranar Litinin.