An kori Harry Redknapp daga Tottenham

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harry Redknapp

Harry Redknapp ya ce yana son samun wani aikin na jagorancin harkokin kwallon kafa bayan da aka sallame shi daga kulab din Tottenham.

An kore shi daga kungiyar ranar Laraba da daddare bayan ya kwashe shekaru hudu yana jagorancinta.

Redknapp ya ce:" Ba zan yi korafi ba.Korafi ba ya cikin abubuwan da nake yi.Ina son wasan kwallon kafa.Zan iya yin kowanne aiki.Don haka ba na tsammani cire ni zai kawo karshen sana'a ta. Shekarun Alex Ferguson 70, amma har yanzu shi ne kocin da ya fi kowa sanin aikinsa.Don haka ba zan karaya ba. ''.

Saura shekara daya kwantaragin Redknapp ta kare a White Hart Lane, sai dai ya ce shugaban kungiyar, Daniel Levy, na son sabon-jini ya jagoranci kungiyar bayan da ta gaza samun nasara a karshen kakar wasa ta badi.

Karin bayani