Hodgson baya fargabar matsin lamba

Kocin Ingila, Roy Hodgson ya nace cewa baya cikin wata fargaba game da irin matsin lambar da 'yan wasansa ke fuskanta.

Ingila za ta buga wasanta na karshe ne a rukunin D, inda za ta taka leda da Ukraine.

"Mun zo gasar nan ne da buri daya, shine mu yi iyakacin kokarinmu domin fita daga cikin rukunin da muke ciki."

Bayan ta samu maki hudu a wasanni biyu da ta buga, Ingila za ta buga wasanta na karshe ne da Ukraine a rukunin D.

Hodgson ya ce: "Ba zamu iya tabbatar da nasara ba, amma muna da kwarin gwiwar cewa zamu taka rawar gani a gasar."

Hodgson zai iya amfani da Theo Walcott a wasansa kasar na gaba bayan dan wasan ya murmure bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta yi nasara a kan Sweden da ci uku da biyu.

Idan har Ingila ta buga kunnen doki da Ukraine a wasanta na karshe, za ta tsallake zuwa wasanni dab da kusa da na karshe.