Hukumar kwallon Kenya ta sallami Kimazi

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kula da kwallon kafa a Kenya ta sallami kocin tawagar kasar wato Francis Kimanzi, da kuma duk masu taimaka masa bayan an fidda kasar a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika ta shekara ta 2013.

Togo ce to doke Kenya da ci daya mai ban haushi a tattakin da kasar ta kai Nairobi, inda Togo din ta yi nasara da kwallon tattaki.

Hukumar kwallo kasar ta ce; " Zamu dauki wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da mahimmacin abin da kuma yasa dole muke sauye- sauye."

Kimanzi dai zai ci gaba da aiki ne da hukumar kwallon kasar, amma a matsayin direktan gudanarwa.

An sake nada Kimanzi ne a watan Nuwamban bara domin ya horar da tawagar kasar a kokarinta na tunkarar wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da na Afrika.

A yanzu haka dai tawagar Harambee Stars ce a kasan tebur a rukunin F, a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekara ta 2014.