Kocin Ingila ya Dogara a kan Rooney

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Wayne Rooney

Kocin Ingila Roy Hodgson na fatan ganin Rooney wanda zai fara bugawa Ingila

wasa a gasar Euro 2012 bayan ya kammala wa'adin dakatarwar da UEFA ta yi

ma sa ya karfafawa sauran 'yan wasan guiwa a wasan da za su yi ranar Talatar

nan da Ukraine.

Dakatarwar da a ka yiwa Rooney din sakamakon rashin da'ar da ya nuna a

Montenegro a watan Oktoba da ya wuce ta sa bai sami damar buga wasan da

Ingila ta yi da Faransa ba inda a ka tashi 1-1 da kuma wanda Ingila ta yi nasara

a kan Sweden da ci 3-2 a wasanninsu na farko a gasar ta Euro 2012.

Hodgson yana duba yiwuwar sanya dan wasan na Manchester United a wasan

na yau tun daga farkon wasan ta yadda zai karfafawa 'yan wasan guiwa.

Ingila ta na bukatar yin canjaras ne kawai ta sami damar zuwa zagayen wasan