Blatter ya jaddada amfani fasahar tabbatar da shigar kwallo raga

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, Sepp Blatter ya jaddada amfani da fasahar tabbatar da shiga kwallo cikin raga bayan da aka samu takkadama a wasan da Ingila ta doke Ukraine da ci daya mai ban haushi.

Kwallon Marko Devic ya wuce layi amma sai alkalin wasan ya ki ya ba da kwallon.

Akwai dai yiwuwar a amince da fasahar tabbatar da shigar kwallo a taron Kungiyar hukumomin kwallon kafa ta kasa da kasa a ranar biyar ga watan Yuli.

"Ganin irin matsalar da aka samu a wasan Ingila da Ukraine, bamu da zabi sai an yi amfani da fasaha mai tabbatar da kwallo ya shiga raga."

Shi kuwa shugaban Hukumar kwallon Turai, Michel Platini ya fi son a rika amfani da alkalan wasa biyar ne a maimakon fasahar.