Shevchenko ya yi murabus daga takawa kasar leda

Hakkin mallakar hoto AP

Andriy Shevchenko bayyana cewa ya yi murabus daga taka ledar kasa da kasa bayan da aka fidda kasarsa a gasar cin kofin Turai.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 35 ya takawa kasarsa leda sau 111, kuma ya buga wasansa na karshe ne a wasan da Ukraine ta sha kashi a hannun Ingila da ci daya mai ban haushi a gasar zakarun Turai.

Shevchenko ne ya jagoranci tawagar kasar inda ta kai wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006.

Dan wasan ya ce zai shirya wani wasan sada zumunci na barinsa kwallon kafa na kasa da kasa.