Ingila na da burin lashe gasar Euro- Hart

Mai tsaron gidan Ingila, Joe Hart ya ce Ingila ba ta gamsu da kaiwa wasan dab da kusa dana karshe ba a gasar Euro.

Tawagar Ingila dai ta yi ba zata a yayinda masu hasashe da dama sun ce ba za ta fito daga rukunin da take ba.

Hart, mai shekarun haihuwa 25, ya ce shi da abokan wasansa suna da kwarin gwiwa za su kara gaba a gasar.

"Dalilin mu na halartar gasar nan ba wai dan mun farantawa mutane rai bane, mun zo ne domin mu lashe gasar." In ji Hart.

Hart ya kara da cewa: "Bama cikin wadanda suke halartar gasar domin kaiwa wasan dab da kusa da na karshe, mun halarci gasar ne domin mu daga kofi kuma mu farantawa mutane Ingila rai."

Ingila dai ta yi nasara ne a wasanni biyu a rukunin C, a yayinda ta buga kunnen doki a wasa daya, kuma a yanzu haka zata buga wasan dab da kusa da na karshe ne da Italiya.