Djokovic ne zai bude gasar Wimbledon

Hakkin mallakar hoto Getty

Na daya a fagen Tennis a duniya, wato zai fara kare kambunsa na gasar Wimbledon ne a wasan farko da za'a fara a gasar ranar Litinin a babban filin wasa.

Dan wasan Tennis din zai kara ne da Juan Carlos Ferrero kuma sannan na ta daya a fagen mata wato Maria Sharapova za ta fafata ne da Anastasia Rodionova.

Na uku a fagen Tennis wato Roger Federer zai hadu ne da Albert Ramos bayan sun gama ne kuma Kim Clijsters itama za ta yi wasa a filin wasa na daya.

Za'a fi maida hankali ne a gasar akan Djokovic saboda shi ya doke Nadal a wasan karshe a shekarar 2011.

A yanzu haka dai Djokovic ne neman kyautar Grand Slam a karo na shida.